Afleveringen
-
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun saâoâi biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya.
Masu kananan sanaâoâi suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sanaâarsu suke lalacewa saboda rashin wuta.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taba rayuwar alâumma da hanyoyin magance ta. -
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san alâadar nan ta bayar da ko karÉo Éa ko âya riĆo.
A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don Ćashin kansu.
Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauĆaĆa danĆon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuÉin sabulu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar âyaâya da iyayen riko. -
Zijn er afleveringen die ontbreken?
-
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su.
Mai yiwuwa wadannan dabiâu ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka.
To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka.
A kan wannan alâada â asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta â shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. -
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai alâumma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga âyan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu.
A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na âyan kasa masu cikakken âyanci, suna da damar kutsawa lungu da saĆo na ko ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai âyan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa mafarautan arewa zuwa kudancin Najeriya yin farauta. -
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura.
Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi.
A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.
-
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana raâayoyinsu kan wannan lamari.
Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar ya dauki wannan mataki, wasu kuwa cewa suke yi ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan ko Doka ta bai wa Shugaban Kasa ikon dakatar da gwamnan jiha da ma 'yan majalisar dokokinta? -
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa.
Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma.
Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo kwararo dauke da ganga da kayan kade kade suna bugawa suna waka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan dadaddiyar aladar, don jin inda ta samo asali, tarihin ta, da kuma yadda ake Gudanar da ita. -
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana â wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.
Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale â ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa.
Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. -
A duk lokacin da aka Éaura aure, wata adduâa da âyan uwa da abokan arziki kan yi ita ce âAllah Ya kawo Ćazantar Éakiâ.
A alâadance, Éaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa.
Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waÉannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. -
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma alâumma?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da âyan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. -
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa.
Sai dai wannan dadaddiyar alâada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan alâada da kuma dalilin gushewar ta. -
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki.
Sai dai wadannan alâadu sannu a hankali suna ta gushewa.
Ko mene ne dalilin wannan sauyin?
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon. -
Son haihuwar âyaâya maza fiye da âyaâya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban.
A tsakanin wasu alâummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar âya mace irin wannan muhimmancin ba.
Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun âyaâya maza a kan âyaâya mata?
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar âyaâya maza a kan âyaâya mata. -
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin alâumma.
Ćorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziĆan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu.
Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musamman a kananan makarantu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari a kan dalilan da suka sa haka. -
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san alâadar nan ta bayar da ko karÉo Éa ko 'ya riĆo.
A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don Ćashin kansu.
Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauĆaĆa danĆon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuÉin sabulu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar âyaâya da iyayen riko. -
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.
Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa âyaâyansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran âyaâyansu da su.
Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a alâadance da ma a addinance?
Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko
-
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.
Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi.
Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka.
-
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti.
Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na kirsimeti ba.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan wannan batu don gano dalilan da suka sa wadannan dariku basa bikin kirsimeti. -
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alĆaryu ta fuskar tsaftar muhalli.
Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baĆi 77 â hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasirinta a kan lafiyar jiki da ta muhalli. -
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da alâummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuriâa ranar Asabar din da ta gabata.
Duk da sauran âyan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zaiyi Nazari ne kan nasarar da John Mahama ya samu a zaben kasar Ghna da kuma kalubalen da zai iya fuskanta a shekara daya na farkon waâadin sa. - Laat meer zien