Afleveringen
-
An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi.
Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. -
Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa.
A bisa alâada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jamiâan lafiya.
Sai dai âyan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jamiâan kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai zube komai a faifai don gano sahihancin wannan zargi da âyan Najeriya suke yi da kuma, idan zargin ya tabbata, yadda aikin jamiâan lafiya ya yi hannun riga da abin da aka karantar da su. -
Zijn er afleveringen die ontbreken?
-
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah.
Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu.
shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin kayan miya suka yi tashin gwauron zabo gabanin bikin Sallah.
-
Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli.
A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace âyan mata goma a Æasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin alâada, saboda rashin kayan tsafta, ruwa da kuma tsaftatattun ban daki.
Irin wannan matsala na addaban mata marasa galihu da wadanda ke zama a karkara.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan irin matsalolin da mata ke fuskanta yayin jinin alâadar su.
-
Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaÉi a jihar, musamman a fannin kiyaye alâada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta.
A baya-bayan nan, hukumar ta fitar da sanarwa inda ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22. Wannan mataki ya biyo bayan saÉani tsakanin hukumar da wasu masu shirya fina-finai, inda hukumar ke zargin cewa fina-finan sun Æetare Æaâidoji.
Sai dai masu shirya fina finan sun bayyana cewa sam hukumar bata da hurumin dakatar da wadannan finafinai.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar tace fina finai ta jihar Kano da kuma masu shirya fina finai masu dogon zango. -
Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa.
Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haÉin kai da zaman lafiya a Æasa.
Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni a ta yadda shugabanci zai rika kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa. -
Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban.
Daya daga cikin nauâukan jarabawa da daliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Sharen Fagen Shiga Manyan Makarantu, wato UTME.
Kamar kowace shekara, a bana ma dalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun samu kasa da maki 200.
Ko wadanne dalilai ne suke kawo faduwa jarabawa a Najeriya?
Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi kokarin amsawa. -
Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da alâadu da halaye na gari a tsakanin Hausawa.
Tatsuniyoyi na Éauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabiâu kyawawa.
Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke shaâawar sauraron tatsuniya ba.
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. -
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun saâoâi biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya.
Masu kananan sanaâoâi suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sanaâarsu suke lalacewa saboda rashin wuta.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taba rayuwar alâumma da hanyoyin magance ta. -
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san alâadar nan ta bayar da ko karÉo Éa ko âya riÆo.
A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don Æashin kansu.
Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauÆaÆa danÆon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuÉin sabulu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar âyaâya da iyayen riko. -
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su.
Mai yiwuwa wadannan dabiâu ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka.
To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka.
A kan wannan alâada â asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta â shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. -
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai alâumma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga âyan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu.
A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na âyan kasa masu cikakken âyanci, suna da damar kutsawa lungu da saÆo na ko ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai âyan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa mafarautan arewa zuwa kudancin Najeriya yin farauta. -
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura.
Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi.
A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.
-
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana raâayoyinsu kan wannan lamari.
Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar ya dauki wannan mataki, wasu kuwa cewa suke yi ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan ko Doka ta bai wa Shugaban Kasa ikon dakatar da gwamnan jiha da ma 'yan majalisar dokokinta? -
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa.
Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma.
Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo kwararo dauke da ganga da kayan kade kade suna bugawa suna waka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan dadaddiyar aladar, don jin inda ta samo asali, tarihin ta, da kuma yadda ake Gudanar da ita. -
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana â wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.
Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale â ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa.
Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. -
A duk lokacin da aka Éaura aure, wata adduâa da âyan uwa da abokan arziki kan yi ita ce âAllah Ya kawo Æazantar Éakiâ.
A alâadance, Éaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa.
Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waÉannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. -
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma alâumma?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da âyan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. -
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa.
Sai dai wannan dadaddiyar alâada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan alâada da kuma dalilin gushewar ta. -
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki.
Sai dai wadannan alâadu sannu a hankali suna ta gushewa.
Ko mene ne dalilin wannan sauyin?
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon. - Laat meer zien